Sabbin ministocin Buhari taron tsintsiyane babu shara, inji PDP

Sabbin ministocin Buhari taron tsintsiyane babu shara, inji PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana sabbin ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar ranar Laraba a matsayin “taron tsintsiya babu shara”, inda ta ce da yawansu na cikin wadanda suka kashe Najeriya a mukamai daban-daban na gwamnati.

Kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan shi ne ya fitar da wannan zancen inda yake cewa, “tarin mutanen da ake tuhuma da laifin cin-hanci da rashawa a matsayin ministoci, shi zai kara tabbatar maku da cewa Buhari bai da wani abinda zai wa Najeriya.”

KU KARANTA:Sabbin Ministoci: Abinda zan soma yi shi ne kawo karshen maganar mafi karancin albashi, inji Ngige

Jam’iyyar adawan ta kara da cewa, “Shugaban kasn ya jima yana goyon bayan cin-hanci da rashawa a fakaice cikin al’amurransa. Haka zalika ya na sanya son ransa wurin bayar da mukamai ba tare ya duba cancanta ba.”

Har ila yau, jam’iyyar PDP ta ce ba ta yi mamakin halin da kasar nan ke ciki ba dangane da mulkin Buhari saboda yadda yake tafiyar da mulkinsa tun wa’adin farko babu wani tsari na musamman.

Kakakin jam’iyyar PDP ya yi magana mai tsawo dangane da ministocin Buhari da kuma yadda yake tafiyar da tsarin mulkinsa, inda ya ce Shugaban kasa ya dade da nuna gazawa wurin jan ragamar Najeriya ba tun yau ba.

Haka zalika, yayi suka a kan batun da Shugaba Buhari ya furta na cewa duk wanda ke son ganawa da shi daga cikin ministocin nasa to kada ya zo masa kai tsaye ya bi ta hannun Abba Kyari wanda shi ne shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, a cewar PDP hakan sam bai kamata ba ga ministocin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel