Fitar da bidiyon Wadume da 'yan sanda su kayi yana ci mana tuwo a kwarya - Kwamitin bincike

Fitar da bidiyon Wadume da 'yan sanda su kayi yana ci mana tuwo a kwarya - Kwamitin bincike

Kwamitin bincike na hadaka da Hedkwatan Tsaro na kasa ta kafa don gano abinda ya faru har ta kai ga kisar 'yan sanda 3 da farar hula a jihar Taraba yayin da sojojin battaliya ta 93 suka bude wa 'yan sanda wuta ta nuna damuwarta kan faifan bidiyon wanda ake zargi, Hamisu Bala da aka fi sani da Wadume.

Jami'an 'yan sanda daga Hedkwatan Rundunar na Abuja ne suka yi nasarar sake kamo Wadume a ranar Talata a jihar Kano.

A cikin faifan bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta da labarai, Wadume ya magantu kan yadda sojoji suka tafi da shi hedkwatansu kafin suka sa mai walda ya cire masa ankwan da ke hannunsa sannan ya tsere.

Wata majiya daga kwamitin binciken ta ce bidiyon na Wadume ya shafawa Hukumar Soji kashin kaza.

DUBA WANNAN: Ganduje vs Abba Gida-Gida: Hukumar INEC ta kammala gabatarwa kotu shaidunta 3

Ya ce abinda ya fi shine a tattauna zancen da ofishin 'yan sanda tunda har yanzu ana gudanar da binciken kan lamarin.

Majiyar da ta nemi a boye sunan ta ta ce: "Mun damu sosai kan sabuwar bidiyon da ta fito da aka nuna wanda ake zargi Wadume yana bayyana kan tserewarsa bayan 'yan sanda sun sake kama shi.

"Duk da cewa mun yabawa 'yan sandan kan sake kamo kasurgumin mai garkuwa da mutanen, bidiyon na Wadume abin damuwa ne duba da cewa ana ta kokarin yin sulhu tsakanin 'yan sanda da sojoji.

"Duk da cewa an bawa kwamitin mu wa'adin mako guda ne ta kammala rahoton ta, an bukaci mu cigaba da aikinmu domin a kammala binciken nan ba da dadewa ba.

"Kama Wadume ya bamu karin haske sosai duba da irin mutanen da aka kama kawo yanzu."

Kwamitin binciken da aka kafa na karkashin jagorancin Rear Admiral Ibikunle Olaiya tana da wakilai daga Rundunar 'Yan sanda, Sojojin Ruwa, Sojojin Sama, 'Yan sandan farar hula, DSS da kuma DIA.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel