Buhari ya kafa ma’aikatar bada agaji, ya maido da wasu tsofaffin Ma’aikatu

Buhari ya kafa ma’aikatar bada agaji, ya maido da wasu tsofaffin Ma’aikatu

Yayin da a ke samun labarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ministocin gwamnatinsa, tare da ba kowane mukamin da zai rike. Mun fahimci cewa an samu sabon cigaba.

A farkon wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya hade wasu ma’aikatu yayin da ya raba wasu da-dama. Wannan karo kuma an yi akasin haka inda har ta kai an kirkiro wani sabon ofis.

Ga jerin sababbin mukaman da a ka kirkiro ko kuma a ka sake dawo da su wannan karo a kasar:

1. Ministar bada agaji da maganin annoba da cigaba

Wannan karo shugaban kasa Buhari ya kafa ma’aikata sukutum da guda da za ta rika lura da bada agaji ga wadanda bala’o’i su ka fada masu. Ma’aikatar kuma za ta yi aikin kawo cigaban kasa wanda a da a ka bar wa Ministar harkokin mata a farkon hawan shugaba Buhari mulki.

Sadiya Umar Faruk wanda ta yi makamancin wannan aiki ne za ta fara jagorantar ma’aikatar.

2. Ministan harkokin ‘yan sanda

Shugaba Buhari ya dawo da ma’aikatar da za ta rika kula da sha’anin ‘yan sanda a Najeriya. A baya an ruguza wannan Ma’aikata inda a ka hada Ministan cikin gida da wannan aiki. Kula da sha’anin tsaro ya sa Mohammed Dangyadi zai zama Ministan 'Yan Sanda a kasar.

KU KARANTA: Buhari ya rika Ma'aikatar fetur bayan ya raba kujerun Ministoci

3. Ministan harkoki na musamman

A wannan gwamnatin, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi aiki da Ministan harkokin musamman a Najeriya. Kafin yanzu an maida wannan ofis karkashin Sakataren gwamnatin tarayya. Sanata George Akume zai jagoranci ma’aikatar bayan ballewar ta daga OSGF.

4. Ministan lantarki

A karshe dai gwamnatin shugaba Buhari ta raba Ma’aikatar wutan lantarki da Ma’aikatar ayyuka da gidaje bayan gama su da a ka yi a karkashin Babatunde Fashola a 2015. Wannan karo Saleh Mamman ne zai kula da sha’anin wutar lantarki inda a ka ragewa Tunde Fashola karfi.

5. Ministan sufurin jiragen sama

Yayin da aka gutsere wani ikon a Ministocin ayyuka da gidaje da kuma Ministar mata, wannan karo an karawa Ministan harkokin jiragen sama matsayi inda ya tashi daga karkashin ma’aikatar sufuri. Hadi Sirika ya samu cikakken 'yanci daga tsohon Maigidansa Rotimi Amaechi.

A wannan karo kuma shugaban kasar ya gama ma'aikatar kasafi da tsare-tsare tare da ma'aikatar kudi. A 2015 ne a ka raba ma'aikatar gida biyu. Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna wanda ta yi aiki a duka ma'aikatun ce za ta cigaba da rike wannan babbar kujera da a ka karawa karfi a 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel