Yanzu Yanzu: Atiku da Buhari: Kotun zaben Shugaban kasa ta jingine hukuncinta

Yanzu Yanzu: Atiku da Buhari: Kotun zaben Shugaban kasa ta jingine hukuncinta

Kotun zaben Shugaban kasa ta ajiye hukuncinta a gefe a karar da Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP) suka shigar inda suke kalubalantar nasarar zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwamitin mutum biyar na kotun zaben Shugaban kasa karkashin jagorancin Justis Mohammed Garba, ya jingine hukuncin zuwa wata rana wanda za a sanar da dukkanin jam’iyyun da karar ya shafa.

Dr Levi Uzoukwu, wanda ya jagoranci tawagar lauyoyin masu kara a jawabin karshe da ya rubuta, yace lallai ikirarin Shugaban kasa Buhari na cewa ya gabatar da satifiket dinsa ga rundunar soji ya fuskanci jayayya daga sakataren hukumar.

Sai dai lauyoyin INEC, Shugaban kasa Buhari da na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sun bukaci kotun zaben da ta yi watsi da karar saboda cewa bai da wani inganci.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2023: Dalilin da ya sa karba-karba ba za ta yiwa APC aiki ba, inji Ganduje

Sun yi korafin cewa dokar kasar ya bukaci dan takara ya kasance da ilimi zuwa matakin sakandar ne kawai.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta kammala tattara bayananta dangane da korafin Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP inda ta roki kotu tayi watsi da karar ta sa.

Lauyan INEC, Yunus Usman (SAN) a lokacin da yake bayyanawa kotu bayanansa ya ce, Atiku ya gabatar da wani zance gaban kotun sauraron karar zaben shugaban kasa inda yake cewa INEC na da shafin yanar gizo wanda take turawa da sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel