Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari, sun kashe da dama

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari, sun kashe da dama

Wasu da 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun kaiwa tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Emmanuel Agbadu Akabe hari inda suka kashe 'yan sanda biyar.

Harin ya faru ne misalin karfe 4 na yamma yayin da mataimakin gwamnan ke hanyarsa na komawa garin Lafiya daga birnin babban tarayya Abuja.

Daily Nigerian ta gano cewa 'yan fashin sunyi kwantar bauna ne inda suka kashe 'yan sanda biyar suka kwashe bindigunsu.

DUBA WANNAN: Atiku ya yi martani kan hukuncin kotun koli na shi duba na'urar INEC

Wata majiya daga jam'ian tsaro ya shaidawa majiyar Daily Nigerian cewa an sanar da tawagar mataimakin gwamnan cewa ana fashi a wani wuri mai suna Lilli kusa da Nasarawa Eggon.

Majiyar ta ce, "Bayan sun jira na dan wani lokaci, daya daga cikin motocin 'yan sanda da ke yiwa mataimakin gwamnan rakiya ya tafi domin korar barayin. Amma sai aka yi rashin sa'a suka fada tarkon 'yan fashin. Suka bude musu wuta suka sace bindigunsu."

Kawo yanzu dai Rundunar 'Yan sanda ba tayi tsokaci kan afkuwar lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel