Atiku ya yi martani kan hukuncin kotun koli na shi duba na'urar INEC

Atiku ya yi martani kan hukuncin kotun koli na shi duba na'urar INEC

- Kotun koli ta hana Alhaji Atiku Abubakar ganin na'urorin zabe na INEC wato server

- Atiku ya daukaka kara ne zuwa kotun kolin bayan rashin amincewar sa da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi

- Atiku ya sakankance kotun sauraran karrakin zaben za ta yi hukunci na gaskiya da adalci

Dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na 2019, Atiku Abubakar ya bayyana cewar tuntuni ya yi hasashen kotun koli za ta hana sa duba uwar-na'urorin INEC.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewar wannan batu ya fito ne ta bakin Eyitayo Jegede (SAN), Mai magana da yawun Atikun.

Jegede ya ce "Kar hankalin kowa ya tashi bisa hukuncin da kotun ta yanke bayan daukaka kara da a ka yi daga kotun daukaka kara".

"An bukaci yin nazari ne a kan uwar-na'urorin zaben na INEC don samun hujja game da magudin da a ka tafka a zaben da ya gabata kamar yadda a ka gabatar a kotun daukaka kara" in ji Jegede.

DUBA WANNAN: Sabon salo: Wadanda suka yi garkuwa da dan limami sun karbi giya a madadin kudin fansa

Wannan bayani ya fito ne bayan sakankancewa da ya yi na cewar kotun kolin za ta tabbatar da gaskiya da adalci.

Shi dai Atiku ya fuskanci kotun kolin ne da bukatar ta kawar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi na kin tursasa INEC da ta ba shi damar duba uwar-na'urorin kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel