Ya zama wajibi mu rika tunawa da nauyin jama’a a kanmu – Boss Mustapha

Ya zama wajibi mu rika tunawa da nauyin jama’a a kanmu – Boss Mustapha

-Sakataren gwamnatin tarayya ya bawa sabbin ministoci wata shawara ta musamman

-Boss Mustapha ya yi kira ga ministocin ne a wurin wani taron tattaunawa da Shugaban kasa ya shirya masu ranar Litinin a Abuja

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya shawarci sabbin ministocin Shugaba Buhari da cewa su kula da tsare amanar al’ummar dake wuyansu.

Mustapha yayi kira ga sabbin ministoci na su yi aiki tukuru a daidai lokacin da zasu kama aiki gadan-gadan a karkashin majalisar zartarwar gwamnatin tarayya.

KU KARANTA:Matashi dan shekara 27 ya zama kwamishina a Jihar Oyo

Sakataren yayi wannan jawabin ne wurin wani taron tattaunawa da Shugaban kasa ya shiryawa sabbin ministocinsa a Abuja ranar Litinin.

Har ila yau, ya tunatar da su aikin gwamnati irin wannan na bukatar hakuri da kuma sadaukarwa saboda nauyin da yake kunshi a cikinsa.

Boss Mustapha yayi kira ga sabbin ministocin ne a cikin jawabinsa na barka zuwa wanda ya gabatar a wurin taron.

Sakataren yayi magana mai tsawo sosai inda yake jan hankalin sabbin ministocin a kan kalubalen dake gabansu na daukan nauyin al’umma a bisa kawunansu.

Bayan gaisuwa da barka da zuwa, sakataren yayi kira ga ministoci cewa kada su manta da amanar mutane ce a hannunsu, ya zamana akwai saudakarwa daga bangarensu musamman a wurin gudanar da ayyukansu.

A wani labarin mai kama da wannan zaku ji cewa, Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya nada dan shekara 27 a matsayin kwamishina.

Kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Adebo Ogundoyin ne ya wallafa wannan labarin a shafinsa na facebook. Matashin mais suna Seun Fakorede tsohon dalibin Jami'ar Obafemi Awolowo ne inda ya samu digirin farko a fannin Civil Engineering a shekarar 2016.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel