Matashi dan shekara 27 ya zama kwamishina a Jihar Oyo

Matashi dan shekara 27 ya zama kwamishina a Jihar Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya zabi wani matashi mai shekaru 27 a matsayin daya daga cikin sabbin kwamishinoninsa.

Matashin mai suna Seun Fakorede ya yi digiri ne a fannin Civil Engineering wanda ya samu daga Jami’ar Obafemi Awolowo wato OAU a shekarar 2016.

KU KARANTA:PDP: INEC ta karawa El-Rufai kuri’un haram a zaben Kaduna

Kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Adebo Ogundoyin ya bada tabbacin zaben matashin a shafinsa na sada zumunta na Facebook a ranar Litinin a cikin wani sako da ya wallafa.

Ga abinda Ogundoyin ya wallafa a shafin nasa, “ Bari mu ba ku wata sanarwa ta musamman, Majalisar dokokin Jihar Oyo ta karbi sunan Seun Fakorede wani matashi mai shekara 27 a cikin sabbin kwamishinonin da gwamnatin Seyi Makinde ta zaba.”

A wani labarin mai kama da wannan kuwa zaku ji cewa, jam’iyyar PDP dad an takararta na gwamna a jihar Kaduna Isa Ashiru Kudan sun bukaci kotu ta rusa wasu kuri’u a zaben gwamnan jihar da ya gabata.

Jam’iyyar PDP da Isa Ashiru Kudan sun a rokon Alkalan da ke sauraron korafin zaben gwamna da aka yi a jihar Kaduna da su soke kuri’u 515,951 da su ke ikirarin cewa bai kamata a tattara da su ba.

A jiya 19 ga watan Agusta, kotu ta sa rana domin ta saurari batun karshe a sahri’ar. A jawabin da jam’iyyar PDP mai korafi za ta gabatar a karshe, PDP za ta bukaci a rusa wadannan kuri’u.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel