Gungun yan bindigan daji sun halaka mutane 17 a jahar Katsina

Gungun yan bindigan daji sun halaka mutane 17 a jahar Katsina

Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a wasu kauyuka guda uku a jahar Katsina a daren Lahadi, 18 ga watan Agusta, inda suka kashe mutane 17, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga mutane 17 da suka mutu, akwai wasu mutane da dama da suka samu munanan rauni a sanadiyyar wannan hari da yan bindigan da suka kai, sa’annan sun yi awon gaba da wasu.

KU KARANTA: Hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna ta tara N17bn a wata 6 – shugaban KDIRS

Yan bindigan sun kaddamar da hare haren ne a kananan hukumomi 3, Safana, Jibai da Danmusa. Yan bindigan sun kashe mutane 4 a kauyen Tsayau dake cikin karamar hukumar Jibia, sa’annan sun kashe mutane 11 a kauyen Danturaki da mutane 2 a kauyen Barza a karamar hukumar Danmusa.

Bugu da kari yan bindigan sun yi garkuwa da mutane 6 a kauyen Zakka dake cikin karamar hukumar Safana, sa’annan sun lalata dukiyoyin jama’a da dama, tare da sace dabbobi.

Al’ummar garin Tsayau sun dauki gawarwakin mutane 3 zuwa fadar mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Jinrin don nuna damuwarsu dangane da cigaba da hare haren da yan bindiga suke kai musu, daga bisani aka yi musu jana’iza a unguwar yan Lihida.

A jawabinsa, shugaban karamar hukumar Danmusa, Sanusi Dangi Abbas ya tabbatar da mutuwar mutane 11. Shima kaakakin hukumar Yansandan jahar Katsina, ASP Anas Gezawa ya bayyana cewa jama’an kauyen sun bi sawun yan bindigan inda suka kwato dabbobinsu, amma yan bindigan sun kashe mutane 4 daga cikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel