Gwamnan Ekiti ya umarci jami’an gwamnati su dinga magana da harshen Yarbanci

Gwamnan Ekiti ya umarci jami’an gwamnati su dinga magana da harshen Yarbanci

Gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi, ya haramta ma kwamishinoninsa da sauran jami’an gwamnatinsa yin magana da harshen Turanci a kowanne irin taro daya danganci al’ada da gargajiya.

Gwamna Fayemi ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta yayin da bikin gargajiya da al’adun jahar daya gudana a garin Ado Ekiti, inda yace ya bada wannan umarni ne don habbaka harshen Yarbanci a tsakanin jama’an jahar.

KU KARANTA: Yaki da cin hanci da rashawa: Babbar jami’a a gwamnatin Buhari ta ajiye aikinta

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jahar Ekiti, Deji Ajayi ya bayyana cewa jahar zata gudanar da gagarumin bikin gargaji da al’adu a watan Disamba na shekarar 2019, inda yace bikin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jahar.

“Daga yau, gwamnati ta haramta yin magana da harshen Turanci a duk wani taro ko hidima daya danganci al’adun gargajiya, don haka duk wanda zai halarci irin wannan taro dolene ya shirya yin magana cikin harshen Yarbanci.” Inji shi.

Da yake jawabi kan maganan baiwa matasa aiki, gwamnan yace gwamnati kadai ba za ta iya baiwa kowa sana’an yi ba, don haka akwai bukatar horas da matasa akan sana’o’in gargajiya na al’adar Yarbawa.

“A lokacin da muka tallata daukan malaman firamari, muna neman Malamai 1,100, amma mutane 19,000 suka nemi aikin, wannan yasa muka fahimci akwai bukatar mu habbaka sana’o’in gargajiya ga matasa ta yadda zasu iya tsayawa dsa kafarsu.

“Sana’o’I kamarsu rawan gargajiya, saka, kira da sauran sanao’in gargajiya. Don haka kada a matsayinmu na iyaye, kada mu manta wajen horas da yayanmu kyawawan dabi’un gargajiya ta yadda ba zasu manta da tahirinsu ba” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel