Maurice Iwu ya koma gida a sakamakon belinsa da a ka biya

Maurice Iwu ya koma gida a sakamakon belinsa da a ka biya

Farfesa Maurice Iwu wanda ya shugabanci hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya ya samu ‘yanci daga gidan yarin da ya ke tsare. Hakan na zuwa ne bayan an biya belin da a ka yanka masa.

Kamar yadda mu ka ji labari, Farfesa Maurice Iwu, ya cika duk sharudan belin da kotu ta gindaya masa inda ya biya kudi Naira Biliyan daya tare da kuma gabatar da mutum biyu wanda za su tsaya masa.

A na zargin tsohon shugaban hukumar zaben ne da laifin cin wasu kudi Naira biliyan 1.23. Wannan ya sa ya shafe mako guda ya na tsare a babban gidan kurkukun nan na Ikoyi da ke cikin jihar Legas.

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta maka Farfesa Iwu a kotu ne da laifin cin wadannan kudi daf da zaben 2015. Alkali mai shari’a Chuka Obiozor shi ne ya bada belinsa.

KU KARANTA: EFCC za ta shiga kotu da wanda ta karbi Biliyoyi a hannun Dasuki

Babban Alkali Obiozor ya nemi wanda a ke tuhuma ya biya Biliyan daya a matsayin beli tare da gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa a kotun. A na bukatar wadannan mutane su mallaki kadara a Legas.

Bayan nan kuma Alkalin da ke sauraron wannan kara ya nemi daya daga cikin wanda zai tsayawa Iwu ya zama babban Ma’aikacin gwamnati wanda ya kai mataki na 16 na aiki ko kuma Farfesa a Jami’a.

Bugu da kari dole ya zamana wadannan mutane sun gabatar da shaidar da ke tabbatar da cewa su na biyan haraji tare da kuma nuna kudin da ke shiga cikin asusunsu. Yanzu dai duk an cika wannan sharuda.

An bukaci tsohon shugaban na INEC ya ajiye fasfon sa na fita kasar waje a hannun kotu. Wannan zai hana shi damar barin Najeriya ba tare da iznin kotu ba. Iwu ya yi wannan kuma an fitar da shi daga gidan yarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel