Alhazai 313 sun daina shan sigari bayan gudanar da aikin hajji a bana

Alhazai 313 sun daina shan sigari bayan gudanar da aikin hajji a bana

Akalla Alhazai 313 ne daga sassa daban-daban na kasashen duniya suka haramta wa kawunansu zukar karan sigari gabanin fara wa da kuma bayan kammala aikin hajji a bana kamar yadda kafar watsa labarai ta Saudi Press Agency SPA ta bayar da shaida.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Alhazai 313 ne daga sassa daban daban na kasashen duniya su ka daina shan sigari bayan sun ziyarci wani asibitin kungiyar Kafa (Enough) dake kasa mai tsarki.

SPA ta ruwaito cewa, shugaban kamfanin Kafa na birnin Makkah, Abdullah bin Dawwod Al-Fayez, shi ne ya bayar da tabbacin hakan a ranar Lahadi.

Ya ce Alhazan a bana sun samu waraka ta kauracewa shan sigari bayan an yi masu magani a asibitin Kafa na garin Mina karkashin jagorancin wata gidauniyar bayar da Sadaka ta Abu Ghazaleh.

Gidauniyar tare da hadin gwiwa ma'aikatar Hajji da Umarah da kuma ma'aikatar lafiya ta kasar Saudiya, suna masu alhakin jagorantar wannan shiri na yaki da shan sigari.

A cewar shugaban kamfanin Kafa A-Fayez, wannan shiri na yaki da sigari ya samo asali ne a karkashin kwamitin wayar da kai a kan illolin shan sigari da masu kula da masallatai biyu mafi alfarma na Makkah da Madinah suka dauki nauyi.

KARANTA KUMA: Kamfanoni 15 da za su rinka shigo da man fetur Najeriya a bana

Shakka babu kwarrarun kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, shan sigari na daya daga cikin miyagun ababe da ke haddasa cutar daji wato Kansa da kuma sauran cututtuka masu alaka da kafofin numfashi a jikin dan Adam.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kimanin mutane miliyan 1.8 ne suka gudanar da aikin hajji a bana da suka hadar da 'yan Najeriya 65,000 da suka ziyarci kasa mai tsarki domin sauke farali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel