Dalilin da yasa muka dawo da El-Zakzaky Najeriya - FG

Dalilin da yasa muka dawo da El-Zakzaky Najeriya - FG

- El-Zakzaky ya fake da zuwa asibiti neman magani ne don ci ma wata mugun manufar sa

- Sakataren Dindindin na Ma'aikatar Labarai da Al'adu, Misis Grace Isu Gekpe, ita ta bayyana hakan.

- Grace ta ce irin rainin hankalin da El-Zakzaky ya nuna su ne su ka sa a ka taso keyar sa zuwa gida Najeriya

A ranar juma'a ne Gwamnatin Tarayya ta fede biri har wutsiya game da maido da El-Zakzaky Gida Nigeria da ta yi. Gwamnatin Tarayya ta bakin sakataren dindindin na Ma'aikatar Labarai da Al'adu da ke Abuja, wato Misis Grace Isu Gekpe, ta ce akwai rainin hankali a da cin mutumcin ta hanyar sharri da kage ga Gwamnatocin Najeriya da na Indiya a lamarin El-Zakzaky.

A cewar Grace, matar El-Zakzaky ta yi wa Gwamnatin Najeriya kazafin kashe ma ta 'ya'ya. Ita kuwa Gwamnatin Indiya, matar ta yi ma ta kagen rashin tausayi da tsanani a gare su, wanda ta fada shi ba don komai ba ne illa don neman tausayi a idon duniya da kuma neman mafaka.

DUBA WANNAN: Wasu boyayyun kananan kasashen duniya 6 da ba kowa ya san su ba

"Al'umma su sani cewar El-Zakzaky ya karya dokokin da a ka gindaya ma sa na barin sa fitar Kasar. Ta kai ga maimakon ya je asibiti, sai ya bukaci a sauke shi a otel mai daraja ta biyar inda zai gana da lauyoyi da kuma kungiyoyin shi'a. An kula cewar ya yi hakan ne don ya samu ya waske zuwa wata kasar don neman mafaka. A takaice dai, zuciyar sa cike ta ke da mugun nufi" in ji Grace.

A cewar Grace, "El-Zakzaky ya fake da zuwa asibiti neman magani ne don ya ci ma wata mummunar manufa ta sa"

"Sakamakon karya wadannan dokoki da kuma cin zarafin Gwamnatocin Najeriya da na Indiya da kuma mugun nufin ya ke kulle da ita ne ya sa babu makawa face a taso keyar sa zuwa gida Najeriya" in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel