Karar Atiku bai da amfani ko kadan – Buhari ga kotun zabe

Karar Atiku bai da amfani ko kadan – Buhari ga kotun zabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana karar da jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar suka shigar, a matsayin mara amfani ko kadan a tarihin zabe.

Shugaban kasar ya bukaci kotun sauraron korafe-korafen zaben Shugaban kasa da ta yi watsi da karar domin bai da tasiri.

Sai dai kuma Atiku Abubakar tare da jam’iyyarsa sun dage kai da fata, atafau shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba tun farko.

Hakan na kunshe ne a jawabin karshe da aka rubuta sannan aka gabatar a gaban kotu, wanda suke sanya ran za a aiwatar a ranar 21 ga watan gusta, lokacin da kotu za ta saurari bayanan karshe daga jam’iyyu akan karar da Atiku da PDP, suka shigar inda suke kalualantar sakamakon zaben Shugaban kasa da ya gabata.

Buhari da APC sun yi korafin cewa baya ga cewar karar da Atiku da PDP suka gabatar bai da ma’ana, sun kuma gaza tabbatar da zarge-zargen kamar yadda yake a cikin kararsu.

KU KARANTA KUMA: El Zakzaky na shirin neman magani a wata kasa bayan Indiya

Buhari da APC, bayan nazari akan hujjar da shaidun masu karar suka bayar, sun yi korafin cewa a kokarinsu na kafa da zarge-zargensu, sun yasar da takardu a kotun da sunan gabatar da hujja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel