Manyan jirage dankaro 15 dauke da man fetir sun shigo Najeriya

Manyan jirage dankaro 15 dauke da man fetir sun shigo Najeriya

Akalla jiragen dankaro 15 dauke da tataccen man fetir da sauran kayayyaki ne suka iso Najeriya ta tashoshin jiragen ruwa guda biyu dake jahar Legas.

Rahotom kamfanin dillancin labaru ta bayyana cewa wadannan tashoshin jirage ruwan sun hada da na Apapa da na Tin Can Island, kamar yadda hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA ta bayyana.

KU KARANTA: Atiku da PDP sun dage kai da fata bai kamata Buhari ya tsaya takara ba tun farko

NPA ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta cikin mujallarta na kowanne rana ‘Shipping position’, inda tace a yanzu a haka jiragen suna jiran a fara sauke kayayyakin da suka yi dakonsu.

Hukumar NPA ta ce daga cikin jiragen guda 15, akwai guda 4 dake dake da man fetir, yayin da sauran 11 sun yi jigilar nau’o’in kayayyaki daban daban ne, sanarwar ta kara da cewa akwai sauran jirage 24 da zasu shigo Najeriya tsakanin 15 zuwa 30 ga watan Agusta.

Daga karshe hukumar ta ce jirage 24 da ake tsammanin isowarsu zasu taho da siga, gishiri, kifi, fulawa, sundukai da kuma hajoji daban daban, sa’annan tace a yanzu haka jirage 18 suna sauke motoci, sundukai, hajoji, man dizil, iskar gas da kuma kifi.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, wanda yan Najeriya suka fi sani da tsohon sunansa ‘NEPA’ daga hannun yan kasuwa don ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da ake fama da shi.

Wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki watau DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya kamata ko kuwa a’a.

Sai dai gwamnatin Najeriya za ta biya yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin rarraba wuta guda 10 naira dala biliyan 2.4 a matsayin kudin fansa, kimanin naira biliyan 736 kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel