Wani Limami ya ci dukan banza bayan an kamashi yana satar wayoyin salula

Wani Limami ya ci dukan banza bayan an kamashi yana satar wayoyin salula

Wani Fasto mai ikirarin da’awa, Akinjide Durojaiye ya gamu da fushin jama’a bayan an kamashi ya saci wasu wayoyin salula guda biyu kirar Tecno daga wani shagon sayar da wayoyi a garin Ibadan.

Wannan lamari ya auku ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta, inda aka kama Faston ya kutsa kai cikin wani shagon sayar da salula dake rukunin shaguna na Femi Johnson a unguwar Dugbe cikin garin Ibadan, hakan tasa jama’a suka suburbudi wannan Fasto, kiris ya rage su kasheshi.

KU KARANTA: Atiku da PDP sun dage kai da fata bai kamata Buhari ya tsaya takara ba tun farko

Sai dai a cewar Fasto Akinjide, yace ya shiga shagon ne da nufin yin da’awar addinin kirista ga dukkanin mutanen dake cikin shagon, ya kara da cewa ruhinsa ne ya karkatar dashi zuwa wannan shago don yin da’awah.

Amma sai ga shi shigarsa shagon da zai yi ‘da’awan’ ke da wuya sai ya suri wasu wayoyi guda biyu da kudinsu ya kai N70,000, amma bai kai ga tserewa ba yaron shagon ya hangeshi, kuma ya saka masa ihun barawo, daga nan jama’a suka bi shi a guje.

A yayin da ake farautarsa, ashe Faston ya shiga cikin wani dakin ajiyan kaya, inda ya boye, amma duk da haka yaron wani shago ya bankadoshi, inda jama’a suka zaroshi daga cikin shagon, suka kwace wayoyin sa’annan suka casa shi ciki da waje.

Fasto Akinjide wanda aka hangeshi yana dauke da ‘Baibul’ ya bayyana cewa sharrin shaidan ne ya kais hi ga aikata wannan aika aika, tare da cewa yana neman kudin da zai kula da lafiyar dansa dan shekara 7, wanda a yanzu haka yake kwance a asibiti a Osun.

Daga karshe jama’an sun kyaleshi ya yi tafiyarsa bayan sun lakada masa dan banza duka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel