Babbar magana: Wasu daga cikin masu bautar kasa ba su iya karanta haruffan turanci – NYSC

Babbar magana: Wasu daga cikin masu bautar kasa ba su iya karanta haruffan turanci – NYSC

Hukumar aikin bautar kasa ta NYSC ta ce za ta mika da wadanda ke ikirarin kammala karatu har ma sun fara bautar kasa amma ba su iya karatun ko haruffan turanci ba.

Darakta Janar na hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ne ya yi wannan magana ranar Alhamis a wata hirarsa da manema labarai. Inda yake cewa duk wani dalibin da yayi karyar yin karatu zai yi shekara biyu a gidan yari.

KU KARANTA:Tsaro: Matawalle ya yiwa Buhari jawabin cigaban da aka samu a bangaren tsaron Zamfara

Har ila yau, Ibrahim ya fadi adadin mutanen da suka yi aikin bautar kasan daga shekarar 1973 da aka kaddamar da shirin zuwa yau, inda ya ce mutane miliyan 4.6 ne suka yi aikin bautar kasan.

Kamar yadda ya ce: “ Mun riga mun sanar da makarantun jami’o’i kan cewa su kula kwarai da gaske kafin turo mana dalibansu da suka kammala karatu.

“ Ina mai sake fadi da babban murya duk wanda muka samu da shahadar kammala karatun digiri na bogi ba zamu yi kasa a gwiwa ba wurin mika shi ga jami’an tsaro. Ba za mu fasa hukunta duk wanda muka samu da irin wannan laifin ba.

“ Abinda zai baka mamaki shi ne, wasu daga cikin daliban da ke ikirarin sun kammala karatun digiri a jami’a idan ka ba su ABCD ba za su iya karantawa ba. Idan na fito maku da takardunsu abin zai matukar baku mamaki.

“ Har wasu ke tambayata ko hukumar NYSC na da hurumin karbe satifiket na wadannan daliban nace da su a’a amma dai zamu iya hanasu yin aikin bautar kasa.” Inji Shugaban NYSC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel