Atiku da PDP sun dage kai da fata bai kamata Buhari ya tsaya takara ba tun farko

Atiku da PDP sun dage kai da fata bai kamata Buhari ya tsaya takara ba tun farko

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar tare da jam’iyyarsa sun dage kai da fata, atafau shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba tun farko.

Atiku ya bayyana haka ne a gaban kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Feburairu, don haka ya nemi kotun ta tabbatar da rashin cancantar Buhari, sa’annan ta tsigeshi daga kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya shiga cikin ruwan sama yayin kaddamar da wasu sabbin hanyoyi 2 a Katsina

Da yake jawabi a gaban kotun, lauyan Atiku, Levy Uzoukwu SAN ya bayyana ma kotun cewa sun tabbatar da magudin da suke zargin an tafka a zaben shugaban kasa, sa’annan sun gabatar da kwararan hujjoji dake tabbatar da zargin da suke yi ma Buhari na rashin mallakan karancin takardar shaidar kammala karatu da ake bukata don tsayawa takarar shugaban kasa.

“Da wannan muke tabbatar ma kotu cewa duk kokarin da Buhari ya yin a nuna mata cewa ya yi karatun sakandari ko na firamari duk a banza ne, saboda bashi da wasu gamsassun hujjoji da zasu tabbatar da hakan.

“Haka zalika kokarin da ya yi na tabbatar ma kotun cewa yana jin turanci kuma yana iya rubutawa shima bashi da amfani tunda dai ya gagara kawo takardar shaidar kammala karatunsa na Firamari, sakandari da kuma sakamakon jarabawarsa ta WASC, sa’annan takardar shigarsa aikin soja ba zai zama hujja ba saboda baya cikin tsarin kundin dokokin Najeriya.

“Me zai sa Buhari ya tafi har Cambridge dake kasar Birtaniya ya amso wani takardar bogi mai dauke da sunansa da sunan wai shine sakamakon jarabawarsa ta WASC, alhalin zai iya zuwa babban ofishin rundunar sojan kasa dake Abuja ya amshi takardun karatunsa?” Inji lauyan Atiku.

Daga karshe Levy ya bayyana ma kotu cewa yadda aka gudanar da zaben 2019 ya saba ma dokokin zaben Najeriya, kuma shaidun da suka gabatar ma kotu sun tabbatar da magudin da aka tafka a zaben, don haka nasarar Buhari haramtacciya ce.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel