Lauya ya shigar da karar neman kotu ta dakatar da rantsar da sabbin ministocin Buhari

Lauya ya shigar da karar neman kotu ta dakatar da rantsar da sabbin ministocin Buhari

Wani lauya mai suna Musa Baba-Panya ya shigar da karar neman wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, daga rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Laraba mai zuwa.

Baba-Panya ya shigar da wannan bukata a gaban kotun ne saboda nuna rashin amincewa da kin saka dan asalin Abuja a cikin sabbin ministocin da shugaba Buhari zai rantsar.

A cikin takardar karar mai lamba kamar haka: FHC/ABJ/CS/878/19 an saka sunan shugaban kasa da babban alkalin gwamnatin tarayya (AGF) a matsayin wadanda ake kara.

Lauyan, wanda shine ya shigar da karar amadadin mutanen asalin Abuja, ya ce rashin saka sunan dan asalin Abuja ya saba wa wani hukunci da wata kotu ta yanke a ranar 15 ga watan Maris, 2018.

Baba-Panya, dan asalin yankin Karu a cikin birnin Tarayya, ya ce yin biyayya ga umarnin kotun ya zama farilla.

"Jerin sunayen ministoci 43 da shugaban kasa ke shirin rantsar wa a matsayin 'yan majalisar bai kammalu ba, a saboda haka ya saba wa doka da kundin tsarin mulki," a cewarsa.

Mai shigar da karar ya roki kotun ta dakatar da shugaban kasa daga rntsar da sabbin ministoci har sai kotu ta fitar da matsaya ta karshe a kan batun.

Ya kara da cewa barin shugaban kasa ya rantsar da sabbin ministocin a haka zai kasance ''tamkar kafa haramtacciyar majalisar shugaban kasa ce."

A cewarsa, tun shekarar 1999 ake ware 'yan asalin Abuja a cikin kunshin nadin mukaman ministoci tare da bayyana cewa lokaci ya yi da zasu taka wa hakan birki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel