Ahmed Kabiru Abdullahi ya samu shiga cikin Gwamnatin Sanwo-Olu

Ahmed Kabiru Abdullahi ya samu shiga cikin Gwamnatin Sanwo-Olu

Ahmed Kabiru Abdullahi ya na cikin wadanda sabon gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya zaba a matsayin Kwamishinoninsa. A na sa ran kwanan nan za a kuma tantance su a majalisa.

Abin sha’awar shi ne Malam Ahmed Kabiru Abdullahi ainihinsa Bahaushe ne. ‘Dan siyasar ya samu shiga cikin gwamnatin jihar Legas tare da wasu sababbin zababbun Kwamishinoni a jihar.

An haifi Kabiru Abdullahi ne a Unguwar Agege a cikin Garin na Legas a 1966. Kwamishinan mai jiran gado ya yi karatun Firamare da Sakandarensa ne tsakanin 1970 zuwa 1985 a cikin Agege.

Sabon Kwamishinan ya yi karatun gaba da Sakandare ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya soma da yin IJMB a 1987 kafin ya kai ga samun Digiri a harkar ilmin zanen gini a 1990.

Ahmed K. Abdullahi yayi Digirgiri watau Digiri na biyu a wannan jami’a a 1992, bayan nan ne ya yi wa kasa hidima. Tun daga wannan lokaci Kabiru Abdullahi ya koma Legas inda ya shiga aiki.

A 1996 Malam Kabiru Abdullahi ya shiga aikin gwamnati gadan-gadan inda har ya yi takarar mataimakin shugaban karamar hukumarsa ta Agege, kuma ta yi nasara ya shiga ofis a shekarar.

KU KARANTA: An sauke Mai ba Buhari shawara kan harkar rashawa daga kujerarsa

Tarihi ya nuna a 1998 ne Abdullahi ya zama Sakataren wata kungiya ta Mutanen Arewa da ke zama a Legas, bayan nan kuma ya zama cikin mutanen farko da su ka kawo jam’iyyar AD a jihar.

Ganin irin kokarinsa ne ya sa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ahmed Kabiru Abdullahi a matsayin shugaban hukumar LASPEMA mai kula da tsarin gine-ginen jihar Legas tun a shekarar 2001.

Sabon kwamishinan ya rike mukamai da dama a LASPEMA har zuwa 2015. A farkon gwamnatin Akinwumi Ambode ne a ka nada shi a matsayin shugaban hukumar LSWRC mai kula da ruwa.

A yanzu kuma gwamnatin Legas karkashin Mai girma Jide Sanwo-Olu ta zabi ta tafi da Ahmed a cikin Kwamsihoninta tare da irin su Yetunde Arobieke, Lola Akande, da Prince Anofiu Elegushi.

Sauran sababbin nadin sun hada da Moruf Akinderu Fatai, Tokunbo Wahab, Solape Hammond, Oladele Ajayi, Oluwatoyin Fayinka, Olanrewaju Sanusi, da kuma Bonu Solomon Saanu, dsr.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel