Dawowa Najeriya: Dalilai 6 da suka Zakzaky barin kasar Indiya ba shiri

Dawowa Najeriya: Dalilai 6 da suka Zakzaky barin kasar Indiya ba shiri

Tun a ranar Laraba, wana biyu bayan ya sauka a kasar Indiya, shugaban kungiyar IMN da aka fi kira da 'Shi'a', Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya fitar da wani faifan bidiyo inda yake korafin cewa gara zama a gidan yarin 'Kirikiri' da zaman asibitin 'Medanta', inda aka kai shi domin duba lafiyarsa.

Sai ga shi a yammacin ranar Alhamis rahotanni sun bayyana cewa Zakzaky ya sallami kansa daga asibitin da aka kai shi tare sallamar kansa da kansa domin ya dawo gida Najeriya.

Dalilai 6 da Zakzaky ya zayyana a kan cewar gara zaman Najeriya da zaman asibitin Medanta na kasar Indiya sune:

1. A cewar Zakzaky, "an kawo mu nan ne domin a duba lafiyar mu. Akwai harsashi har yanzu a jikin mata ta, Zeenat, akwai bukatar a fitar da shi sannan a canja mata murfin kokon gwuiwar ta guda biyu.

Ni ma ina fama da matsalar ido da ta guba, wacce aka ce ta shiga har cikin kashin jikina, a saboda haka aikin fitar da ita zai dauki lokaci."

2. ''Jami'an Asibiti sun yaudari magoya baya na'': A cewar Zakzaky, an hada baki tare da jami'an asibitin da za a kwantar da shi ta hanyar yin amfani da wata mota, sabanin wacce ya kamata, wajen fitar da shi daga filin jirgin sama zuwa asibitin ta wata barauniyar hanya yayin da magoya bayansa ke jira a bakin kofar filin jirgin domin su tarbe shi.

3. Zargin ana son hallaka shi: Zakzaky ya bayyana cewa ba zai yarda wani ma'aikacin asibitin ya kasance cikin masu duba lafiyarsu ba sai wadanda suka zaba da kansu. Ya yi zargin cewa likitocin da aka zaba su duba shi, zasu aikata abin da hukumomin Najeriya suka kasa yi da harsashin bindiga.

4. Gara zaman gidan yarin 'Kirikiri' da zaman asibitin: Zakzaky ya yi korafi a kan cewa an saka masa matakan tsaro masu tsanani a asibitin, matakan da ya bayyana cewa zasu shafar lafiyar kwakwalwarsa.

"Ko dakin da ke kusa da ni sun ki su barni na leka. Ko lokacin da nake garkame a Najeriya ban fuskanci tsaro mai tsanani kamar wannan ba. Karfe 9:00 na dare ake rufe mana daki a wurin da aka tsare mu a Najeriya, sannan a bude mana kofa karfe 7:00 na safe, kuma muna iya zagaya wa a tsakanin dakunan yankin da muke tsare. Amma a nan lamarin ba haka yake ba, tun da muka zo suke matsa mana, bamu da wani sukuni," a cewar Zakzaky.

5. Ba zamu iya yarda da Indiya wa ba: Daga cikin kalaman Zakzaky ya bayyana cewa ba zasu iya yarda da Indiya wa ba, musamman na asibitin da aka kwantar da shi.

6. Zargin saba wa yarjejeniya: Zakzaky ya zargi gwamnatin Najeriya da saba wa yarjejeniyar da aka kulla a kan likitocin da zasu duba lafiyarsu kafin su bar Najeriya.

A cewarsa, akwai yarjejeniyar cewa sai likitocin da suka zaba ne suka duba su, amma bayan an je kasar Indiya sai gwamnatin ta canja baki tare da saba wa yarjejeniyar da aka kulla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel