Yanzu Yanzu: Sheikh El-Zakzaky zai dawo gida Najeriya

Yanzu Yanzu: Sheikh El-Zakzaky zai dawo gida Najeriya

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, na a hanyarsa na dawowa Najeriya daga asibitin Indiya inda ya je yin magani.

Kakakin kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa, ya tabbatar wa manema labarai cewa shugaban na Shi’a zai dawo Abuja da karfe 5:00 na yamma.

Har ila yau, a cewar wani rubutu da aka wallafa a shafin Twitter daga ofishin Zakzaky, ana sanya ran shugaban kungiyar na IMN zai iso Abuja da karfe 17:00.

Wani bidiyo da aka wallafa tare a shafin Twitter ya kuma nuno El-Zakzaky yana bayanin cewa asibitin Indiya ta amince za ta bari ya dawo Najeriya tare da matarsa Zeenat, biyo bayan rikicin da ya barke kan zabi na likitocin da za su kula da su da kuma ka’idojin jinyan.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya.

Kawo yanzu babu bayani a hukumance daga mahukuntan Indiya ko kuma na Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Hazikan sojoji 3 sun kwanta dama yayinda suka dakile harin Boko Haram a kauyen Borno

Idan za ku tuna dai tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa, sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan mummunar halayyar da ya nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel