To fah: Shugaba Buhari ya ce zai kawo karshen talauci a Najeriya, yayin da kuma ya bayyana bangaren da zai ba wa muhimmanci a wannan karon

To fah: Shugaba Buhari ya ce zai kawo karshen talauci a Najeriya, yayin da kuma ya bayyana bangaren da zai ba wa muhimmanci a wannan karon

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen talauci a Najeriya da kuma karfafa fannin noma

- SHugaban kasar ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kudurin da yake dashi a wannan zangon nashi karo na biyu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma bukaci matasan Najeriya da su kara kaimi a fannin noma inda ya ce shine jigon arziki a kowacce kasa ta duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudurinsa na kawo karshen bakin talaucin da ke faruwa a kasar nan, sannan kuma ya kawo cigaba ga talakawan kasar.

Da yake magana a ranar Talatar nan 13 ga watan Agusta, a lokacin da ya karbi bakuncin manyan shugabannin kananan hukumomin Daura guda biyar.

Da yake yiwa 'yan Najeriya godiya akan sake zaben shi da suka yi, shugaban kasar ya bayyana cewa wannan zangon zai yi amfani dashi wajen cika alkawuran da ya dauka lokacin zabe akan tattalin arziki da tsaro.

KU KARANTA: Tirkashi: Sabon rikici ya barke tsakanin Muneerat Abdulsalam da mawaki Misbahu M Ahmad

Ya ce: "Kowa ya san abinda na sanya a gaba. Kuma haka zabe ya nuna, gwamnatina za ta fara aiki akan alkawuran da muka dauka, irinsu matsalar tsaro, tattalin arziki, da cin hanci da rashawa. Za mu yiwa talakawa aiki a wannan karon."

Shugaban kasar kuma yayi alkawarin sanya mutumin kirki a matsayin ministan gona, domin amfani da wannan bangaren wajen samawa 'yan Najeriya aiki.

Haka kuma ya sha alwashin inganta rayuwar manoman Najeriya domin samun abinci mai yawa a Najeriya. Sannan ya bayyana cewa ya ji dadin yadda matasan Najeriya suka dage a fannin noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel