Boko Haram: Rundunar soji ta canja babban kwamandan rundunar 'Ofireshon Lafiya Dole'

Boko Haram: Rundunar soji ta canja babban kwamandan rundunar 'Ofireshon Lafiya Dole'

A kokarin ta na kara karfin yakin da take yi da aiyukan kungiyar Boko Hara a yankin kudu maso gaba, rundunar sojin Najeriya ta sanar da nada sabon kwamanda da zai jagoranci wata babbar rundunar atisaye da ke Maiduguri, jihar Borno.

Birgediya Janar AK Ibrahim, kwamanda (GOC) a runduna ta 7 da ke Maiduguri, jihar Borno, ya zama sabon kwamandan runduna ta 1 a karkashin atisayen 'Ofireshon Lafiya Dole'.

A cewar wata wasika da ta fito daga ofishin sakataren rundunar soji, birgediya janar Ibrahim zai karbi aiki ne daga hannun manjo janar Bulama Biu, wanda ke jagorantar rundunar atisayen da ma runduna ta 3 ta sojojin hadin gwuiwar kasashen gefen tekun Chadi (MNJTF)

Sabon canjin ya fara aiki ne daga ranar Laraba,14 ga watan Agusta, 2019.

Kazalika an sanar da yi wa manjo janar CG Musa da BA Akinroluyo canjin wurin aiki zuwa sashen sojoji (TRADOC) da ke Minna, jihar Neja.

Ko da yammacin ranar Alhamis, saida Legit.ng ta wallafa wani labari a kan rahotanni sun kawo cewa sojoji uku sun mutu a lokacin da dakarun Operation lafiya dole suka dakile harin yan ta’addan Boko Haram a kauyen Molai da ke jihar Borno.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi, sun gudu (Hotuna)

Dakarun sun fafata da yan ta’addan a wani musayar wuta da suka yi a daren ranar Laraba, 14 ga watan Agusta a Mammanti, wani kauye kusa da Maiduguri, babbar birnin jihar.

Yan ta’addan wadanda suka fito da yawa na a hanyarsu na kai farmaki Molai, kilomita biyu daga babbar birnin jihar kafin su fara musayar wuta.

Karar tashe-tashen bama-bamai da alburusai a tsakar dare ya jefa mazauna Molai da wasu yankunan Maiduguri cikin wani hali.

Sojoji a fadin Mammanti wadanda ke shirn shiri, su fuskanci yan ta’addan, inda suka dakile shirye-shiryensu na shiga Molai.

Musayar wutan wanda ya fara da misalin karfe 10:00 da dare ya kai har karfe 2:30 na tsakar dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel