'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi, sun gudu (Hotuna)

'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi, sun gudu (Hotuna)

Wasu barayi sun fasa na'urar fitar da kudi (ATM) tare da satar kudi masu yawa da ba a san adadinsu ba.

'Yan sanda sun ce Barayin sun fasa ATM din ne a wani hari da suka kai da safiyar ranar Laraba a Southampton, kasar Ingila.

Babu wanda ya san adadin kudin da suka sata a ATM din, wanda ke wajen wani shago dake wata tashar gefen hanya.

Kakakin rundunar 'yan sanda a yankin Hampshire ya bayyana cewa, "muna rokon dukkan wasu masu shaida a hannu a kan wadannan barayi da ya sanar da hukuma.

DUBA WANNAN: Kanu Nwankwo ya samu mukami a sabuwar gwamnatin PDP a jihar Imo

"Mun tura jami'an tsaro yankin kuma sun samu na'urar da aka cire, da kuma gurbin da aka kwashe kudin da ke wurin da aka cire na'urar ATM din.

"Mutane da dama sun kira ofishin mu tare da bayyana cewa sun ji karar fashewar wasu sinadarai a daidai lokacin da Barayin suka kai harin.

"Duk mai wani muhimmin bayani zai iya tuntubar mu."

'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi, sun gudu (Hotuna)

'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi
Source: Facebook

'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi, sun gudu (Hotuna)

'Yan fashi sun fasa ATM sun kwashi kudi
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel