Nadin Ministoci: Buhari ya sabawa kundin tsarin mulki kasa - Lauya

Nadin Ministoci: Buhari ya sabawa kundin tsarin mulki kasa - Lauya

Mazauna kuma 'yan asalin babban birnin kasar nan na tarayya, sun nemi babbar kotun kasa dake garin Abuja da ta dakatar da rantsar da zababbun ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Biyo bayan nadin ministoci 43 tare da tantance su da majalisar dattawa ta yi a watan Yuli, shugaban kasa Buhari ya kayyade ranar 21 ga watan Agusta a matsayin ranar rantsar da su tare da ratayawa kowanensu makamar aiki ta ma'aikatun gwamnati da za su jagoranta.

Sai dai cikin wani korafi a madadin mazauna garin Abuja da wani lauya Musa Baba Panya ya gabatar gaban kotun a ranar Alhamis, ya nemi da a haramtawa shugaban kasa Buhari rantsar da ministocinsa a sanadiyar rashin zaben minista ko da guda daya dan asalin garin Abuja.

Lauyan ya ce shugaban kasa Buhari ya sabawa hukuncin da babbar kotun daukaka kara ta zartar a watan Janairun 2018 wadda ta tilasta masa zabar minista dan asalin garin Abuja.

Panya ya ce a sanadiyar yiwa kundin tsarin mulkin kasa karen tsaye har karo biyu tare da sabawa alkawali na nauyin shugabancin kasar nan, shugaba Buhari bai cancanci ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar ba.

KARANTA KUMA: Ganduje ya rabawa Alhazan Kano naira dubu biyar-biyar

Ya kuma nemi kotun da ta tursasawa Buhari biyan diyyar naira miliyan 500 sakamakon sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma biyan naira miliyan 10 a matsayin kudin shigar da korafi gaban da rataya a wuyan shugaban kasa da kuma lauyan kolu na Najeriya.

Alkali da ya jagoranci zaman kotun, mai shari'a Taiwo Taiwo, ya sanya ranar Litinin ta mako mai zuwa domin fara sauraron korafin da kuma zartar da hukunci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel