Hazikan sojoji 3 sun kwanta dama yayinda suka dakile harin Boko Haram a kauyen Borno

Hazikan sojoji 3 sun kwanta dama yayinda suka dakile harin Boko Haram a kauyen Borno

Rahotanni sun kawo cewa sojoji uku sun mutu a lokacin da dakarun Operation lafiya dole suka dakile harin yan ta’addan Boko Haram a kauyen Molai da ke jihar Borno.

Dakarun sun fafata da yan ta’addan a wani musayar wuta da suka yi a daren ranar Laraba, 14 ga watan Agusta a Mammanti, wani kauye kusa da Maiduguri, babbar birnin jihar.

Yan ta’addan wadanda suka fito da yawa na a hanyarsu na kai farmaki Molai, kilomita biyu daga babbar birnin jihar kafin su fara musayar wuta.

Karan tashe-tashen bama-bamar da alburusai a tsakar dare ya jefa mazauna Molai da wasu yankunan Maiduguri cikin wani hali.

Sojoji a fadin Mammanti wadanda ke shirn shiri, su fuskanci yan ta’addan, inda suka dakile shirye-shiryensu na shiga Molai.

Musayar wutan wanda ya fara da misalin karfe 10:00 da dare ya kai har karfe 2:30 na tsakar dare.

Ba a san adadin mutanen da suka mutu ba ta bangaren yan ta’addan, amma majiyoyin sojoji sun bayyana cewa an kashe sojoji uku a arangamar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An bayar da belin surukin Atiku kan N20m

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, kakakin Operation Lafiya Dole, Kanal Ado Isa, bai yi sharhi ba.

Kanal Isa bai amsa kiran waya ko sakon da ke neman Karin bayani kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel