'Yan bindiga sun sace 'yar uwar wani babban dan siyasa a Sokoto

'Yan bindiga sun sace 'yar uwar wani babban dan siyasa a Sokoto

'Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wata mata mai dauke da juna biyu, Luba Bello.

Rahotanni sun ce matar 'yar uwar wani fitaccen dan siyasa ne a garin Denge da ke karamar hukumar Shuni a jihar Sokoto.

Tana barci a gidan ta tare da iyalanta ne lokacin da 'yan bindigan suka afka musu misalin karfe 2 na dare a Denge inda suka yi wa maigidanta duka kafin su kayi awon gaba da ita.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky ya saba dokokin belinsa a India - FG

A yayin da ya tabbatar da afkuwar lamarin, Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Sadiq Abubakar ya ce an kira ofishin 'yan sanda da ke Dange Shuni inda aka fada musu cewa mutane 7 dauke da bindigu sun kai farmaki kauyen Latura misalin karfe 2 na dare sun sace wata mata mai juna biyu.

Abubakar ya ce, "A halin yanzu da na ke maka magana, 'Yan sanda suna bin sahun masu garkuwa da mutanen domin ceto matar. 'Yan sanda sun kammala bincika dajin da ke kusa da garin kuma an fara gudanar da bincike kan lamarin."

Ya kara da cewa za ayi duk mai yiwuwa domin ganin an ceto matar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel