Yadda Buhari ya shiga cikin ruwan sama yayin kaddamar da wasu sabbin hanyoyi 2 a Katsina

Yadda Buhari ya shiga cikin ruwan sama yayin kaddamar da wasu sabbin hanyoyi 2 a Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sabbin hanyoyi guda biyu a yankin Dauran jahar Katsina, sai dai Buhari ya gudanar da kaddamawar ne yayin da ake tsaka da zuba ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Buhari ya kaddamar da hanyoyin ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta, inda ya kaddamar da titunan da suka tashi daga Fago-Katsayal-Kwasarawa-Jirdede-Koza, dukkaninsu cikin masarautar Daura.

KU KARANTA: Yadda wani matashi mai halin bera ya debo ruwan dafa kansa daga satar waya

Sai dai a yayin da yake gudanar da kaddamarwar, sai shugaban kasa Buhari ya ankara cewa jami’an Sojojin dake bashi tsaro a wajen suna sanye da rigar kare ruwa, watau ‘Rain Coat’ yayin da jami’an Yansandan basu sanye da rigar kare ruwa, hakan tasa suka jike sharkaf.

Nan take ba tare da bata lokaci ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya juya ya kalli babban jami’an Dansandan dake cikin yan tawagarsa mai mukamin AIG, inda ya tambayeshi:

“Ya ka bar jami’anku ba tare da rigunan kare ruwa ba?” ai kuwa sai wannan AIG ya yi zugum yana kallon Buhari, ba uhm ba uhm uhm, wai uwar gulma ta yi cikin shege.

Ganin haka ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tunkarar babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu a kan rashin kyautata ma jami’an Yansanda.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Buhari na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, wanda yan Najeriya suka fi sani da tsohon sunansa ‘NEPA’ daga hannun yan kasuwa don ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da ake fama da shi.

Wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki watau DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya kamata ko kuwa a’a.

Sai dai gwamnatin Najeriya za ta biya yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin rarraba wuta guda 10 naira dala biliyan 2.4 a matsayin kudin fansa, kimanin naira biliyan 736 kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel