Kanu Nwankwo ya samu mukami a sabuwar gwamnatin PDP a jihar Imo

Kanu Nwankwo ya samu mukami a sabuwar gwamnatin PDP a jihar Imo

Tsohon dan wasan Najeriya da ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Indiya, Kanu Nwankwo, ya samu mukamin babban mai bawa gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, shawara a kan harkokin wasanni.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Izuchukwu Akwarandu, sabon mai taimakawa gwamna a bangaren yada labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa; "gwamna Emeka Ihedioha ya karbi bakuncin daya daga cikin jaruman 'yan wasan kwallon kafa na kasa, Kanu Nwankwo, a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri, a ranar 14 ga watan Agusta, 2019.

"Papilo, kamar yadda masoyansa ke kiransa, ya gabatar da kyautar dan wasan kwallon kafa na nahiyar Afrika (CAF) da ya lashe, wacce kuma aka bashi bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika a kasar Misra. Ya ziyarci gwamnan ne domin gabatar masa da kyautar saboda soyayyar da yake nuna wa mutanen jihar Imo.

DUBA WANNAN: Miji, mata da 'ya'yansu biyu sun mutu bayan cin tuwon Sallah a Kebbi

"Kazalika, ya bawa gwamna kyautar wata rigar wasa ta musamman.

"A yayin da yake gabatr da jawabi godiya da maraba ga Kanu da 'yan rakiyarsa, gwamna Ihedioha ya sanar da Kanu cewa ya nada shi a matsayin babban mai bashi shawara a kan harkokin wasanni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel