Yadda 'Yan sanda suka kama matar da ta kulle yaro a kejin kare

Yadda 'Yan sanda suka kama matar da ta kulle yaro a kejin kare

Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta kama wata mata da aka dauki hoton ta tana dukan wani maraya mai shekara 10 kuma ta rufe shi a kejin karnuka.

Jaridar Punch ta gano cewa lamarin ya faru ne a unguwar Surulere da ke jihar Legas.

Bidiyon ya tayar da hankulan mutane a shafukan sada zumunta, har wasu suka yi alkawarin bayar da lada ga duk wanda ya taimaka aka gano inda matar take.

'Yan Najeriya da dama sun kuma bukaci hukumomin tsaro su zabura domin kama matar da kuma gurfanar da ita gaban kuliya domin fuskantar shari'a kamar yadda Mai magana da yawun 'yan sanda Dolap Badmus ta bayyana.

DUBA WANNAN: Matar da ta bugawa 'yar ta guduma a goshi ta fuskanci fushin kotu

A rubutun da ta wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, Badmus ta ce an kama matar da ake zargi.

Ta ce, "A makon da ta gabata mun samu rahoton cewa wata mata ta yi wa wani yaro duka ta jefa shi a dakin karnuka.

"Mun zaburar da jami'an mu masu binciken cin zarafin bil adama a gida kuma sun kamo matar.

"Za a gurfanar da matar a kotu. Yaron da kuma aka gano maraya ne yana hannun gwamnatin jihar Legas ana kulawa da shi."

An gano cewar wani makwabcin matar ne ya dauki hoton bidiyon a sirrance.

Daga bisani matar da kuma bayyana cewa yaron sha wani abin sha ne daga firinji sannan baya jin magana, ta kara da cewa yaron 'ya'yan ta ne da mahaifansa ya rasu aka ba ta shi riko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel