Yanzu Yanzu: An bayar da belin surukin Atiku kan N20m

Yanzu Yanzu: An bayar da belin surukin Atiku kan N20m

Justis Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke Lagas a ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta, ya bayar da belin Abdullahi Babalele, surukin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ya bayar da belin nasa ne akan kudi naira miliyan 20 tare da wanda zai tsaya masa mutum guda.

Alkalin ya bayyana cewa dole wanda zai tsaya masa ya zama mazaunin jihar Lagas sannan kuma ya gabatar da hujja ta hanyar daukar rantsuwa a rubuce.

An umurci Babalele da ya gabatar da fasfot dinsa, wanda ke a hannun kotun.

A baya mun ji cewa hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC ta gurfanar da Babalele Abullahi, surukin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar a gaban kotu.

An gurfanar da Babalele ne a safiyar ranar Laraba gaban mai shari'a Nicholas Oweibo na Babban Kotun Tarayya da ke Legas bisa tuhumarsa kan aikata laifuka biyu masu alaka da satar kudade.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: El-Zakzaky ya sake magana daga kasar Indiya (bidiyo)

Sai dai bai amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Justice Oweibo ya bayar da umurnin EFCC ta cigaba da rike Babalele a hannun ta har zuwa gobe Alhamis da za a saurari bukatar bayar da shi beli da lauyansa Mike Ozekhome (SAN) ya nema kotun ta bayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel