Kwadayi mabudin wahala: Saurayin da ya damfari budurwarsa naira miliyan 4.5 ya shiga hannu

Kwadayi mabudin wahala: Saurayin da ya damfari budurwarsa naira miliyan 4.5 ya shiga hannu

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun yi ram da wani macuci tare da gurfanar dashi gaban wata kotun majistri dake zamanta a jahar Legas, inda suke tuhumarsa da damfarar budurwarsa kudi naira miliyan 4.5.

Haka zalika rahoton jaridar Punch ta bayyana saurayin mai suna Obinna Amaefula da ya yi ikirarin shi dan kasuwa ne ya dirka ma budurwarsa tasa Ese Odobo ciki, kuma ya yi mata yan dabarbaru ya zubar mata da cikin dan wata biyar.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari zai kwace NEPA daga hannun yan kasuwa, zai mayar musu da kudinsu

Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Lucky Ihiehie ya bayyana ma kotu cewa Obinna ya aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Mayu a gidansu dake rukunin gidaje na Atunrase, a unguwar Gbagada dake jahar Legas.

“Obinna ya amshi naira 4,550,000 daga hannun budurwasa Ese Odobo da sunan zai sayo mata motoci guda yan kwatano don amfani dasu a kasuwancinta, alhali ashe ya san karya yake sharara mata, daga nan kuma ya ci gaba da yi mata karairayi a kan dalilin rashin zuwan motocin.

“Daga wannan lokaci ne budurwar ta ankara cewa damfararta saurayinta ya yi, amma a lokacin data tunkareshi da maganan, sai ya shiga dukanta yana marinta, duk da cewa ya san tana dauke da cikinsa wata 5, bayan wasu yan kwanaki kuma ya sanya mata kwaya a cikin lemu, ta sha, cikinta kuma ya zube.” Inji shi.

Da wannan ne Dansandan ya nemi kotu ta hukunta wanda ake kara daidai da laifin daya aikata, wanda hakan ya saba ma sashi na 171, 287, 236 da 314 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015.

Sai dai saurayin ya musanta wadannan tuhume tuhume guda hudu da suka danganci sata, cin zarafi da kuma damfara, amma duk da haka Alkalin kotun, Ejiro Kubeinje ya aika dashi gidan kaso har zuwa ranar 28 ga watan Agusta don cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel