Tashin hankali: Wata mata ta yiwa saurayin 'yarta wanka da tafasashen ruwa bayan ta yaudareshi ya je gidanta

Tashin hankali: Wata mata ta yiwa saurayin 'yarta wanka da tafasashen ruwa bayan ta yaudareshi ya je gidanta

- An cafke wata mata da ta yiwa wani saurayin 'yarta wanka da ruwan zafi bayan ta yaudareshi ya je ziyara gidanta

- Tun farko dai dama matar ba ta kaunar saurayin 'yarta ta tun lokacin da suka fara soyayya

- Lamarin ya faru ne bayan mahaifiyar yarinyar ta roke shi yaje gidanta domin suyi magana ta fahimta, da zuwanshi ta watsa mishi tafasashen ruwa

Jami'an 'yan sanda sun kama wata mata da ta watsawa saurayin 'yarta ruwan zafi bayan ta yaudareshi yaje gidanta.

Legit.ng ta gano cewa mahaifiyar budurwar ba ta kaunar saurayin ko miskala zarratun tun lokacin da ya fara soyayya da diyar tata.

Amma kuma ana haka sai kwatsam sai mahaifiyar yarinyar ta kirashi, inda ta nemi yaje gidanta domin suyi magana ta fahimta.

KU KARANTA: To fah: An kama wani dan sanda da ya dinga surfawa shugaba Buhari da Osinbajo zagi a shafin Facebook

Da zuwanshi gidan, sai tayi masa sallama da ruwan zafi cikin tukunya, inda kuma ta koma yi masa ihun barawo.

Yanzu dai an yi gaggawar garzayawa da saurayin asibiti mafi kusa, inda ita kuma mahaifiyar budurwar aka kama ta domin hukunta ta akan laifin da tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel