Canzawa gidan yarin Najeriya suna ya yi daidai inji Shehu Sani

Canzawa gidan yarin Najeriya suna ya yi daidai inji Shehu Sani

Mun samu labari cewa fitaccen Sanatan da ya wakilci yankin tsakiyar jihar Kaduna a majalisa ta takwas watau Shehu Sani, ya fito ya yabawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu yabon tsohon Sanatan ne bayan da ya fara shirin canzawa gidajen kurkuku suna. Yanzu za a rika kiran su gidan gyara dabi’a a Najeriya.

A cikin makon nan mu ka samu rahoto cewa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wani kudiri da majalisar tarayya ta kawo masa wanda zai kawo sauyi a gidajen yarin kasar.

Sanata Shehu Sani wanda ya saba yin magana kan batutuwan kasar ya fito ya shafinsa na kafafen yada labarai ya na jinjinawa wannan mataki da shugaban kasar ya dauka a makon nan.

KU KARANTA: An damke Jami'in da ya ke zagin Shugaban kasa da Osinbajo zagi a Facebook

Tsohon ‘dan majalisar ya ke cewa: “Canza sunanan gidan yari zuwa gidan gyara dabi’a a Najeriya, abu ne mai kyau.” Sanatan ya cigaba da jawabi ya na mai bada shawara kuma cewa:

“Yanzu abin da ya rage shi ne gwamnati ta tabbatar cewa wadannan gidajen kaso sun ci sunan su.” Kwamared Sani ya na nufin ya zamana gyaran da a ka ce a ke yi a gidan mazan.

Jama’a da dama su na ganin cewa tsohon Sanatan ya saba sukar gwamnatin shugaba Buhari. Sai dai ko a kwanan nan ya yaba da tsarin hana bada kudi domin shigo da abinci Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel