JAMB ta ba Attahiru Jega mukami, zai shugabanci kwamitin daukar dalibai a jami’a

JAMB ta ba Attahiru Jega mukami, zai shugabanci kwamitin daukar dalibai a jami’a

Hukumar jarrabawata JAMB ta bayyana cewa an nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban kwamitin harkokin da suka shafi bai wa dalibai damar shiga manyan makarantun jami'a a Najeriya.

Farfesa Emeritus, Olugbemiro Jegede, tsohon shugaban jami’ar 'National Open University of Nigeria' ne zai zama mataimakin Jega.

Sauran mabobin kwamitin na mutum tara sun hada da; tsohon shugaban jami'ar Noma ta tarayya, Fafesa Olushola Oyewole, tsohon shugaban jami'ar Uyo, Farfesa Comfort Ekpo, Farfesa Aminu Mikailu, Farfesa Domwini Kuupole da kuma tsohon shugaban kungiyar jami'o'in Afrika ta yamma (AWAU), Farfesa Adenike Oladimeji, Fasasi Zubairu.

Yayin da ake kaddamar da kwamitin, Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede yace kaddamar da kwamitin ya zama dole, domin inganta manyan cibiyoyin karatu a kasar, don haka akwai bukatar samar da kayan aiki cikin gaggawa domin cimma manufar shirin daga 2019/2020.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da ya sa APC ta dakatar da Abdulmumini Jibrin

Kwamitin da Jega ke jagora zata samar da dabaru don inganta tsarin shiga manyan jami'o'in Najeriya ta hukumar JAMB.

Kwamitin har ila yau tana da alhakin samar da shawarwari ga cibiyoyin JAMB a kasashen waje don janyo hankulan dalibai, musamman yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, da su nemi shiga jami’o’in Najeriya tare da samar da sabon tsarin gudanar da jarrakaratabawar shiga manyan makarantun kasar a kasashen waje da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel