APC za ta cigaba da mulkar Najeriya har bayan 2023, inji Kakakin Majalisar Nasarawa

APC za ta cigaba da mulkar Najeriya har bayan 2023, inji Kakakin Majalisar Nasarawa

- Ibrahim Abdullahi, Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta cigaba da mulkar Najeriya bayan 2023

- Abdullahi ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yi wa jam'iyyar APC da Najeriya shiri mai kyau

- Kakakin Majalisar ya ce Shugaba Buhari mutum ne da ba zai kakabawa 'yan Najeriya mutumin da ba sa kauna ba

Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa, Ibrahim Abdulllahi ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) za ta cigaba da mulkan Najeriya har bayan shekarar 2023 saboda irin ayyukan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi a kasar.

Abdulllahi ya fadi hakan ne a ranar Laraba 15 ga watan Augusta a kauyensu na Umaisha da ke Jihar Nasarawa yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Abdullahi ya ce: "A lokacin da wa'adin mulkin Buhari za ta kare, ina tabbatar maka cewa duk wanda zai biyo bayanshi zai cigaba da irin ayyukan da fara ne saboda irin ingantattun ayyuka da ya ke yiwa kasa da jam'iyya.

"Buhari mutum ne da ba zai kakabawa mutane wanda ba su kauna ba a 2023.

"Za muyi nazarin mutane bisa mizanin nagarta kuma duk wanda muka amince zai iya maye gurbin Buhari, za mu mara masa baya.

"Saboda haka, ina tabbatar maka da cewa APC za ta cigaba da mulkin Najeriya har bayan 2023, babu shakka a hakan."

Abdullahi ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi wa Buhari addu'a kuma su mara gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule baya a yunkurin su na magance kallubalen tsaro da ake fuskanta a jihar da kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel