Ku sauya salon yaki da ta’addanci, Buhari yayi kira ga shugabannin tsaro

Ku sauya salon yaki da ta’addanci, Buhari yayi kira ga shugabannin tsaro

-Shugaba Buhari ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijarar Batsari ta jihar Katsina

-Shugaban kasan ya kira ga shugabannin hukumomin tsaro da su kirkiro sabbin hanyoyin yakar ta'addanci domin share hawayen 'yan Najeriya kan tabarbarewar tsaro

Shugaban kasan Najeriya yayi kira ga shugabannin hukumomin tsaron Najeriya da cewa su sauya salon yadda suke yakar ta’addanci domin samun sakamako mai kyau.

Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi wannan maganar ne a ranar Laraba yayin da ya kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira wato IDP dake karamar hukumar Batsari a Jihar Katsina.

KU KARANTA:Obono-Obla: Dalilin da yasa Buhari ya tsige shi

A cewarsa an mika wannan sakon ne zuwa ga dukkanin shugabannin hukumomin tsaro a wurin wata ganawar hukumomin tsaro wadda ta gudana a cikin makon da ya wuce.

Ya bada tabbacin samar da tsaro ga ‘yan gudun hijiran, inda ya ce masu gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta domin ganin cewa al’ummar kasar nan sun zauna cikin kwanciyar hankali.

Ya sake cewa, babu wani mai aikata irin wadannan munanan laifuka da zai kwana lafiya matukar ya shigo hannun hukuma. Tsare rayukan al’ummar kasar nan shi ne muradin gwamnatinmu, a cewar Shugaba Buhari.

Kakakin shugaban kasan, Malam Garba Shehu ya tsakura daga cikin zancensa inda yake cewa: “ Ina cike da takaicin halin da wannan tsaron ya jefa ku ciki, babu damar yin ayyukan kawao cigaba ta fannin tattalin arziki a kauyukanmu.”

“ Haka zalika, noma wanda shi ne ake yiwa kirari da tushen arziki ya gagaremu a yau. Amma kada ku damu ina samun jawabi dangane da tsaro daga wurin Gwamna Aminu Bello Masari kuma zamu sake mayar da hankali a kan yankunan da abin yafi shafa.” Inji Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel