Ya kamata yan Najeriya su mara wa ajandar Next Level din Buhari baya - APC

Ya kamata yan Najeriya su mara wa ajandar Next Level din Buhari baya - APC

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Lagas, Cif Lanre Razak, ya bukaci yan Najeriya da su nuna goyon bayansu ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin taimaka masa wajen inganta kokarin da yayi a mulkinsa na farko.

Razak ya yi rokon ne a wani hira da manema labarai a Lagas inda ya nuna karfin gwiwar cewa “ajandar Next Level na Shugaban kasar gaskiya ce ba wai karya ba,” inda ya bayyana cewa “wasu matakai da Buhari ya dauka ya tabbatar da cewar yana kokarin isar da dukkan alkawaran da ya daukarwa al’umma.

“Bayan lura da cewar matsalolin tsaro a kasar na da alaka da waje da kuma goyon bayan wasu yan kasar waje, Shugaban kasar ya hadu da shugabannin kasashen da ke makwabtaka tare da kudirin fitar day an ta’adda daga kowani yanki na kasar,” inji Razak.

A cewarsa, wannan mataki kari ne akan ganawar da ake da dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar kamar shugabannin addini, shugabannin kabilu, hukumomin tsaro da sauran shugabanni na kasar, cewa “Wannan ya nuna cewa Buhari a matsayinsa na shugaba yana dauke da kasar a zuciya.

KU KARANTA KUMA: Ali ya ga Ali: Yadda ziyarar Shugaban Guinea ta hada Ganduje da Sarki Sanusi har sau 6

“Ya Najeriya su ci gaba da godiya ga Allah da ya bamu Muhammadu Buhari a lokacin da kasar ke bukatar wani mai ceto.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel