Obono-Obla: Dalilin da yasa Buhari ya tsige shi

Obono-Obla: Dalilin da yasa Buhari ya tsige shi

-Shugaba Buhari ya sauke Obono-Obla daga kan mukaminsa

-A daren jiya Laraba ne fadar shugaban kasan Najeriya ta fitar da bayanin sallamar Obla tare da ba shi umarnin cewa ya kai kansa zuwa ga ICPC

-Daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da shi akawai na yin amfani da sakamakon WAEC na jabu

A daren jiya ne Fadar Shugaban kasa ta fitar da zancen tsige Cif Okoi Obono-Obla daga bisa mukaminsa na jagorancin kwamitin bincike na musamman game da dukiyar da aka kwato daga hannaun barayin gwamnati.

Sai dai har yanzu, jama’a da dama na cigaba da tsegumi a kan dalilin da yasa aka sauke wannan mutumin daga mukaminsa.

KU KARANTA:Sojoji sun bankado wani haramtaccen kamfanin sarrafa bindiga a Binuwe

Wata majiyar da ta fito daga fadar shugaban kasa ta ce akwai badakkalar takardun makaranta da kuma zargin cewa ya wawure wasu makudan kudade.

Majiyar ta bamu labarin cewa: “ Ofishin ministan shari’an Najeriya ya aminta da a dakatar da jagoran tare da gudanar da bincike na musamman a kan zargin da ake yi masa.

“ Haka zalika, fadar shugaban kasa ta samu wani labari game da shugaban hukumar inda ake cigaba da zuzuta maganar cewa takardunsa na jabu ne.

“ Obla na da laifuka da dama wadanda ake tuhumarsa da cewa ya aikata. Akwai wawure kudin ofis, amfani da takardun karatu na jabu da kuma saba dokokin aikin su kansu.

“ A shekarar da ta gabata akwai makamanciyar wannan maganar a gaban wata kotun daukaka kara. A wancan lokacin kotun ba ta samu gamsassun hujjojin karbe masa ababen da ya mallaka ba.

“ Kotu a wancan lokacin umarni da ta bayar ga kwamitin binciken Obla shi ne su koma domin sake tattaro bayanai na hakika wanda zai taimakawa kotu wurin warware wannan badakkalar.” A cewar majiyar.

Bugu da kari Obla yayi amfani da karfin hukumar da yake jagoranta wurin rage karfin ikon EFCC da ICPC a wurin wasu ayyukansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel