Ali ya ga Ali: Yadda ziyarar Shugaban Guinea ta hada Ganduje da Sarki Sanusi har sau 6

Ali ya ga Ali: Yadda ziyarar Shugaban Guinea ta hada Ganduje da Sarki Sanusi har sau 6

Kamar yadda Hausawa ke fadi, wani na cin albarkacin wani, hakan ce ta kasance tskanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II. Babu wanda ya kawo a kai cewa za su hadu a lokacin bukukun Sallah fiye da sau guda.

An yi zaton za a sake komawa gidan jiya, a sake shata layi tsakanin bangarorin biyu a cikin lokacin bikin sallah, lokacin da masarautar Kano ta aike wa duka hakimai takardar cewa su kai dawakinsu Kano domin yin hawa.

Sai dai gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen fitar da wata sanarwa tana umartar duka hakiman jihar su tafi sababbin masarautunsu su yi hawan sallah a can, wanda hakan a fili mataki ne na kalubalanatar umurnin masarautar Kano.

A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A lokacin hawan na karamar sallah dai manyan jam'ian gwamnati sun je kallon hawa a sabbin masarautun a matsayin manyan baki, sai dai babu wanda ya je kallon hawan Sarki Sanusi da sunan gwamnatin Kano.

Daga baya dai wasu manyan mutane da suka hada da Alhaji Aliko Dangote da shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi sun shiga tsakani inda suka yi wani zaman sulhu tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano.

Abin da ake ganin ya taimaka wajen yayyafa wa kurar da ta taso ruwa.

Mutane da dama sun yi zaton rigima za ta sake komawa sabuwa, bayan masarautar Kano ta aikewa hakima wasika cewa su halarci hawan sallah a Kano, yayin da ita kuma gwamnati ta fitar da sanarwa tana umartar kowane hakimi ya yi sallah a masarautar da yankinsa ta fada.

To sai dai a iya cewa abubuwan da suka faru sun bai wa kowa mamaki, ganin yadda gwamnan da sarkin Kano suka hadu sau shida daga ranar Lahadi da aka yi sallah, zuwa ranar Talata da aka yi hawan Nasarawa.

A kowace rana dai shugabannin sun hadu sau biyu a wurare da lokuta daban-daban, abin da ba wanda ya taba zaton hakan zai faru a nan kusa.

KU KARANTA KUMA: To fah: An kama wani dan sanda da ya dinga surfawa shugaba Buhari da Osinbajo zagi a shafin Facebook

A lokacin hawan, Sarki Sanusi ya jadadda cewa zai ci gaba da ba gwamnatoci hadin kai, sannan ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da bai wa gwamnatoci goyon bayan kan abubuwan da suka shafi ci gaban al'umma.

A nashi bangaren gwamnan Kano ya yi nuni da tamkar babu wata matsala tsakanin bangarorin biyu.

A yayin jawabin dai babu inda gwamnan ya ambaci sabbin masarautun jihar, haka kuma ba a ga ko da daya daga sauran sarakunan na Kano masu daraja ta daya a wajen hawan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel