Sojoji sun bankado wani haramtaccen kamfanin sarrafa bindiga a Binuwe

Sojoji sun bankado wani haramtaccen kamfanin sarrafa bindiga a Binuwe

-Dakarun sojojin OPWS sun kama wani mutum dake sarrafa bindigogi a haramtaccen kamfani

-Kwamandan sojin Manjo Adeyemi Yekini ne ya bada wannan labarin ga manema labarai a ranar Laraba

-Yekini ya bada labarin cewa mutum goma aka kama a jihohin Binuwe da Nasarawa da laifuka daban-daban

Dakarun sojojin dake karkashin Operation Whirl-Stroke a ranar Laraba sun gano wani haramtaccen kamfanin sarrafa bindigogi a karamar hukumar Buruku dake jihar Binuwe.

Kwamandan tawagar sojin wacce akeyiwa inkiya da OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini ne ya shaidawa ‘yan jarida wannan labarin.

KU KARANTA:Karyane babu yaron da aka kona a Kaduna, inji ‘yan sanda

Yekini ya ce mutum goma ne suka samu damar kamawa, 6 daga Nasarawa yayin da sauran hudun kuma daga nan jiharsu ta Binuwe.

“ Makonni uku da suka wuce munyi wani zama na tattaunawa inda aka kawo mana mutum 8 da jami'an suka kama. Sai ga shi kuma yau din nan da rana mun sake gabatar da wasu mutum 10 wadanda ke da alaka da manyan laifuka irinsu fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a jihohin Nasarawa da Binuwe.” Inji Kwamandan.

Daga cikin wadanda aka Kaman akwai, Saidu Muhammadu wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane tare da yaran aikinsa mutum biyu. Akwai Moses Dzever rikakken dan bindiga ne wanda ke kungiyar Terwase Akwaza wadda jami’an tsaro suka dade suna farauta.

Har ila yau, akwai Shekwa Terna wanda shi ne mai kamfanin sarrafa bindigogin. Da yake hira da manema labarai Terna bai musanta laifin nasa ba, inda ma yake cewa shekaru biyar da suka wuce ya fara koyon wannan harkar da wurin babban wansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel