To fah: An kama wani dan sanda da ya dinga surfawa shugaba Buhari da Osinbajo zagi a shafin Facebook

To fah: An kama wani dan sanda da ya dinga surfawa shugaba Buhari da Osinbajo zagi a shafin Facebook

- Wani dan sanda da ya yiwa shugaba Buhari, Osinbajo da shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Mohammed Adamu kudin goro ya zaga ya shiga hannu a jiya Laraba

- Dan sandan ya bayyana cewa Najeriya cike take da azzaluman shugabanni wadanda babu abinda suke yi sai zaluntar talakawansu

- Ya bayyana cewa a shirye yake ya mutu yana fadar gaskiya da ya zauna yana kallon wannan abin bakin cikin da bacin rai a kasar nan

Wani dan sanda da yake aiki a karkashin hukumar 'yan sanda ta jihar Yobe, an kama shi saboda ya zagi shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo da kuma shugaban hukumar 'yan sanda na kasa Mohammed Adamu a shafin Facebook.

Jami'in dan sandan wanda aka bayyana sunansa da Sunday Japhet yayi zargin cewa mugayen mutane ne suke mulkar Najeriya a ranar 9 ga watan Agustan nan a shafinsa na Facebook. Ya kuma bayyana cewa jami'an hukumar 'yan sanda zasu fara gabatar da zanga akan albashinsu wanda wasu mutane suka ajiye a cikin wani asusu domin su dinga samun riba.

KU KARANTA: Ga irinta nan: Wani mutumi ya mutu a daidai lokacin da yake zina da wata bazawara a cikin gonar masara

Japhet yayi rubutu kamar haka:

"Wannan ita ce Najeriyar da shugaban kasarta zai yaki cin hanci ya kuma kawo karshen matsalar tsaro, da mataimakinsa wanda yace shi mai tsoron Allah ne, da sanatoci da kuma shugaban hukumar 'yan sanda da muke tunanin zamu samu canji daga bangarenshi, duka ina tausaya musu. Ina addu'ar wannan zanga-zangar da za ayi a ranar 14 ga watan Agusta a jihohin Borno, Yobe, Adamawa da sauran wurare, ina fatan 'yan sandan da aka sanya su aiki na musamman ba za su yi ba saboda hanasu alawus dinsu da aka yi.

"Muna kira ga duka 'yan jarida da su halarci wannan waje na zanga-zanga, wadannan mutanen da suke kiran kansu da shugbanni sun san da cewa albashinmu yana cikin asusun wasu tsirarun mutane kawai don suna so su samu riba, sai bayan wata 3 ko hudu sai su biya mutane, babu wanda ya isa ya ce bai san abinda ke faruwa ba a kasar nan. Allah zai yi mana sakayya idan har wannan shine Buharin da yake mulkar Najeriya, gwanda na mutu ina fadar gaskiya da na zauna ina kallon bakin ciki da bacin rai."

Kwamishinan 'yan sanda jihar Yobe, Sunmonu Adeyemi Abdulmaliki ya tabbatar da cewar an kama dan sandan a jiya Laraba 14 ga watan Agustan nan. Kwamishinan ya bayyana cewa an mayar dashi jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel