Za a binciki kisan Faston Najeriya da a ka yi a Sin - Inji Dabiri-Erewa

Za a binciki kisan Faston Najeriya da a ka yi a Sin - Inji Dabiri-Erewa

Mun samu rahoto cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci a yi bincike na musamman bayan kashe wani Malami mai suna Joseph Nwajueze. Wannan abin takaici ya faru ne a kasar China.

Marigayi Joseph Nwajueze, Fasto ne wanda asalinsa ‘Dan Najeriya ne amma ya tare a can kasar China. A na zargin cewa jami’an tsaron kasar ta China ne su ka hallaka wannan Bawan Allah.

Shugabaar hukumar NIDCOM ta ‘Yan Najeriya da ke zaune a kasar waje, Madam Abike Dabiri-Erewa, ta nemi a yi bincike domin gano duk diddikin abin da ya faru domin a dauki mataki.

Dabiri-Erewa ta ce dole a gudanar da bincike na musamman a game da kisan wannan Malamin addini. Shugabar ta NIDCOM ta kuma ce akwai bukatar a hukunta wanda a ka samu da laifi.

Wannan Malamin addinin Kirista haifaffen jihar Anambra ne a Kudu maso Gabas. Abike Dabiri-Erewa ta ce Joseph Nwajueze yana zama ne tare da Maidakinsa Chinwe da ‘Ya ‘yansu hudu.

KU KARANTA: Buhari ya fatattaki Obono-Obla bayan gano ya na aiki da takardun karatun bogi

Abdur-Rahman Balogun wanda shi ne Mai magana da yawun bakin Abike Dabiri-Erewa, ya bayyana cewa a na zargin jami’an tsaron kasar Sin din su ka kashesa a kan takardun shiga kasar.

Rahotanni sun ce Marigayin ya yi yunkurin tserewa jami’an kasar wajen ne a dalilin rashin takardun biza, a sanadiyyar haka ne a ke zargin Ma’aikatan wannan kasa su ka kashe shi har lahira.

Hadimin shugabar ta NIDCOM, Balogun, ya ke cewa babu dalilin kashe wannan Bawan Allah. A wannan jawabin har wa yau, an yi Allah-wadai da yadda a ke kyamatar ‘yan Najeriya a kasar.

Misis Dabiri-Erewa ta yi wa Iyalin Fasto Nwajueze ta’aziyya tare da tabbatar masu da cewa za a hukunta wanda su ka kashe shi. An kuma nemi ’Yan Najeriya da kar su dauki doko a hannunsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel