Shugaba Buhari ya shiga sansanin ‘Yan gudun hijira a Batsari

Shugaba Buhari ya shiga sansanin ‘Yan gudun hijira a Batsari

A Ranar Laraba, 14 ga Watan Agusta, 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da mutanen da ke cikin sansanin IDP a dalilin rikicin da ya rutsa da su a wasu Yankunan Katsina.

Shugaban kasar ya gana da mutane 1, 050 da ke cikin sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Batsarin jihar Katsina. A nan ne a ke ajiye da wadanda rikicin jihar ya barke da su.

Rikicin garkuwa da mutane da satar kayan Bayin Allah ya ci kananan hukumomi akalla takwas da ke Katsina musamman ta yankin Dajin rugu. Yanzu an kafa sansanin IDP a cikin Garin Batsari.

Mun samu rahoton shugaba Buhari ya ce: “Ina matukar bakin cikin halin da wadannan Miyagu su ka jefa jama’a, wanda ya taba yanayin tattalin arziki da kuma zamantakewar wadanda ke nan.

Shugaban kasar ya ke cigaba fadawa wadannan mutane cewa: “An yi wa harkar noma da jama’a su ka dogara da shi illa. Ina so ku san cewa gwamnatin tarayya ta san da halin da ku ke ciki”

KU KARANTA: Shugabannin APC da Buhari ba su halarci bikin Oyegun ba

“Ina samun rahotan duk abubuwan da ke faruwa kullum daga jami’an tsaro da kuma gwamna Aminu Masari wanda ya same ni ta-ka-nas ya mani bayanin kashen-kashen da a ke yi.” Inji Buhari.

Daga cikin hanyoyin da gwamnati ta ce ta ke bi wajen kawo karshen wannan rikici shi ne amfani da fasaha wajen gano wadannan Miyagu. Mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya fadi wannan.

Shugaban kasar ya yi kira ga jama’a su tashi tsaye da addu’a su dafawa jami’an tsaro. Buhari ya ce akwai wasu bata-gari ne a cikin jama’a da ke ba wadannan Miyagu da ke ta’adi bayanan da su ke samu.

Shugaban kasar ya kuma godewa wadanda ke taimakawa da gudumuwa irin su Maidakinsa Hajiya Aisha Buhari, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Dahiru Mangal da kuma bankin nan na Stanbic IBTC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel