Gwamna Sule zai biya kudin filin jami'ar NOUN da albashinsa na Yuni da Yuli

Gwamna Sule zai biya kudin filin jami'ar NOUN da albashinsa na Yuni da Yuli

Mai girma gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya hakura da karbar albashinsa na watannin Yuni da Yulin bana domin a saye filin da za a gina jami’ar nan NOUN a jiharsa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust a Ranar 14 ga Watan Agusta, 2019, gwamnan ya yafe albashin na sa ne saboda a biya kudin filin da za a shimfida ginin wannan babbar jami’a.

Jami’ar nan ta National Open University of Nigeria (NOUN) za ta gina babban sashenta ne na jihar Nasarawa a cikin Garin Lafia. Gwamnan ya bayyanawa jama’a wannan a cikin makon nan.

Sule ya ke fadawa shugabannin jami’ar cewa: “Kun yi sa’a ba a biya ni albashin Watannin Yuni da Yuli ba, za a biya ni kudin ne a lokaci guda, don haka zan saya maku filin daga albashi na.”

KU KARANTA: Matar Gwamnan Kadunat rabawa Bayin Allah abincin sallah

Gwamna na Nasarawa ya kara da: “Wannan shi ne zai zama gudumuwa ta domin ganin an kawo cigaba a harkar ilmi. Kamar yadda na saba fada, zan taimakawa bangaren ilmi ta duk hanyar da zan iya.”

Shugabannin jami’ar sun nemi a daga masu kafa ne su yanki filin da za a gina makarantar a jihar inda gwamnan ya nuna cewa ba zai yi haka ba a daidai lokacin da ya ke kukan jihar na naman kudin shiga.

Shugaban jami’ar NOUN na reshen jihar Nasarawa, Farfesa Alachi James Atu ya yi magana a wajen wannan taro da a ka yi a gidan gwamnati. Gwamnan zai bada gudumuwar kudi fiye da Miliyan 1.3.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel