Liverpool ta lashe kofin UEFA Super Cup

Liverpool ta lashe kofin UEFA Super Cup

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta doke Chelsea 5-4 a bugun da kai sai mai tsaron gida bayan da wasan nasu ya gagara karewa a cikin mintuna 90.

An buga wannan wasan ne babban birnin kasar Turkiya wato Istanbul a daren Laraba. Wasan ya tashi ne da ci 2-2 bayan an buga karin lokaci na tsawon minti 30 babu wanda yayi nasara, hakan ne ya sadasu zuwa bugun da kai sai mai tsaron gida.

KU KARANTA:Karyane babu yaron da aka kona a Kaduna, inji ‘yan sanda

Cikin ‘yan wasa goma da suka doka bugun da kai sai mai tsaron gida tara sun jefa kwallon cikin tsare sai dan wasan Chelsea daya Tammy Abraham wanda ya ba mai tsaron gidan Liverpool kwallon a hannunsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel