Karyane babu yaron da aka kona a Kaduna, inji ‘yan sanda

Karyane babu yaron da aka kona a Kaduna, inji ‘yan sanda

-Hukumar 'yan sandan Kaduna ta karyata labarin cewa an kona wani yaro da ransa a jihar

-Kakakin hukumar 'yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ne yayi watsi da wannan maganar inda ya ce karya ce tsagwaronta

-Kwamishinan 'yan sandan Kaduna ya ci alwashin hukunta masu yada ire-iren wadannan labaran

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna tayi fatali da labarin dake yawo a kafafen sada zumunta na cewa wai an kona wani yaro dan kabilar Igbo da ransa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Janga shi ne ya fitar da wannan jawabin ta bakin kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ranar Laraba.

KU KARANTA:Bidiyo: Wani gogaggen matsafi ya fito cikin bukka bayan ta kone kurumus

Zancen ya ce an wallafa wannan labarin ne a shafin Nairaland Forum, wata kafar sadarwa dake watsa labaranta a yanar gizo.

Wanda ya wallafa labarin ya boye cikakken bayanin mutanen da abin ya shafa da kuma wurin da abin ya faru.

“ A don haka hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna ke kiran dukkanin al’ummar Kaduna da ma Najeriya baki daya cewa su yi watsi da wannan labari saboda zancene maras tushe.

“ Masu rubuta irin wannan labarin na karya na yin hakan ne domin su haifar da tashin hankali a tsakanin jama’a wanda kan iya kasancewa a rikicin kabila ko kuma na addini.

“ Hukumar har ila yau tayi gargadi ga masu yada ire-iren wadannan jita-jita da su yi gaggawar tuba idan kuma bah aka ba fushin hukuma zai hau kansu.” Inji Kakakin hukumar.

Janga ya fadi da babbar murya cewa, hukumar ‘yan sanda za ta hukunta duk wanda ta samu da laifin yada labaran kanzon kurege musamman wanda zai iya haifar da tashin-tashina a jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel