Kisan 'yan sanda: An gano wata takarda dake nuni da yadda rikici ke neman barkewa tsakanin 'yan sanda da sojoji

Kisan 'yan sanda: An gano wata takarda dake nuni da yadda rikici ke neman barkewa tsakanin 'yan sanda da sojoji

- Wata takarda da aka gano ta bayyana yadda shugaban hukumar soji ya dinga yiwa jami'an tsaro gargadi akan yanayin aiki

- Shugaban ya bukaci jami'an tsaro na ciki da wajen kasar nan da su guji sanya kansu cikin matsala

- Wata majiya ta bayyana cewa an nemo wannan takarda ne domin a kawo matsala a tsakanin hukumomin tsaron kasar nan

Wani rubutu da aka gano daga wajen shugaban hukumar soji na Najeriya Lt. Gen. Tukur Buratai, ya bayyana yadda yake gargadin jami'an hukumar soji akan yadda suke tafiyar da al'amuransu tsakaninsu da jami'an hukumar 'yan sanda akan kisan 'yan sandan da ya faru a jihar Taraba.

A jikin takardar da shugaban hukumar sojin ya sanyawa hannu, ya umarci duka rundunar soji dama duka jami'an tsaro da suke ciki da wajen kasar nan su guji duk wata hanya da zata sanya su cikin matsala.

"Dole shugabanni da kwamandojin sojoji su koyar da jami'ansu akan yadda zasu dinga tafiyar da lamuransu tsakaninsu da 'yan sanda."

KU KARANTA: Wata sabuwa: Najeriya za ta tarwatse kuma 'yan arewa ne za su ji jiki - Sheikh Gumi

Amma wata majiyar ta bayyana cewa an sanya wannan rubutu ne a kafar sadarwa domin a kawo matsala ga hukumomin tsaro na kasar nan.

Majiyar tace sai dai idan har gwamnatin tarayya ta yi da gaske, shine har za ta kawo karshen matsala dake tsakanin hukumomin guda biyu.

Tuntuni hukumar tsaro ta kasa ta sanya wata kwamiti wacce za ta gabatar da bincike akan matsalar wacce Rear Admiral I T Olaiya yake shugabanta, ya kuma samu wakilai daga hukumomin tsaron soja, sojan ruwa, sojan sama, 'yan sanda, 'yan sandan farin kaya da dai sauransu.

Haka shima shugaban hukumar 'yan sanda na kasa ya sanya kwamitin bincike, wacce mataimakin shugaban hukumar yake jagoranta domin gano inda matsalar take akan kisan 'yan sanda uku da aka yi a garin Takum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel