Zan saka wa sabbin ministoci ido tare da yi musu gwaji da jarrabawa - Buhari

Zan saka wa sabbin ministoci ido tare da yi musu gwaji da jarrabawa - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke shirin rantsar da ministocinsa a mako mai zuwa ya bayyana irin tanadin da yayi wa majalisarsa ta Next Level.

Buhari ya bayyana cewa za a sanar da dukkanin ministocin ayyukansu da manufofin da ke tattare da ayyukan gami da abunda ake tsammani daga gare su.

Har ila yau Shugaban kasar yace ofishin babban sakataren gamnatin tarayya za ta sanya idanu sosai akan ministocin domin ganin kamun ludayinsu.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta.

“Ministoci masu zuwa, wadanda za a rantsar a mako mai zuwa, za su ga cikakken manufofi da ke tattare da ayyukansu.

“Za mu tabbatar da ganin cewa an bi ka’idojin manufofin,sannan ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya za ta sanya idanu sosai akan kokarinsu.”

KU KARANTA KUMA: Mutanen da ke kashe bayin Allah sannan suna ihun Allahu Akbar makaryata ne - Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai yi amfani da wa’adin mulkinsa na biyu wajen yi ma talakawan Najeriya yaki ta hanyar ianganta rayuwarsu, tare da zama garkuwa a garesu daga sharrin azzalumai.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 13 ga watan Agusta a garin Daura yayin da al’umman kananan hukumomin masarautar Daura guda biyar suka kai masa ziyarar Sallah a gidansa, inda yace ya gamsu cewa yan Najeriya sun fahimci aniyarsa, shi yasa suka sake zabensa a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel